Jamus ta lallasa Ingila a gasar cin kofin duniya

Jamus 4 Ingila 1

Jamus ta lallasa Ingila da ci hudu da guda a gasar cin kofin duniya dake gudana a kasar Afrika ta kudu.

Kafin a tafi hutun rabin lokaci dai an tashi wasan ne Jamus na da kwallaye biyu, Ingila na da guda.

Dan wasan Jamus Miroslav Klose ne ya fara zura kwallon farko ana minti ashirin da fara wasan , sanan Lukas Podolski ya zura ta biyu ana minti talatin da biyu.

Dan wasan bayan Ingila Mathew Upson ya fanshe kwallo guda ne kafin a tafi hutun rabin lokaci amma dai Frank Lampard dai ya buga kararrawa inda kwallon ya wuce layi amma dai alkalin wasan ya ki bada kwallon.

Bayan an dawo hutun rabin lokaci ne dai, Thomas Mueller ya zurawa Jamus kwallonta na uku a minti sittin da bakwai. Sanan kuma bayan minti uku dan wasan ya zura ta hudu.