Ghana za ta buga wasan dab da kusa da na karshe

Ghana 2 USA 1
Image caption Ghana 2 USA 1

Ghana ta doke Amurka da ci biyu da guda a gasar cin kofin duniya da ke gudana a kasar Afrika ta kudu a zagaye na biyu.

Ghana dai yanzu haka za ta buga wasan dab da kusa dana karshe ne da Uruguay wanda itama ta doke Koriya ta kudu da ci biyu da daya.

Ghana ce fara zura kwallon farko a wasan, kafin Amurka ta fanshe, sannan kuma da aka shiga karin lokaci bayan minti casa'in na wasa Ghanan ta samu ta zura na biyu.

Ghana dai ta kafa tarihi a gasar cin kofin duniya, a matsayin kasar Afrika ta uku da ta kai wasan dab da kusa dana karshe bayan Kamaru da Senegal.