An sabunta: 28 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 10:44 GMT

Holand 2-1 Slovakiya

Holland ta doke Slovakiya

Holland na jiran wanda zai fito tsakanin Brazil da Chile

Haland ta doke Slovakiya da ci biyu da daya a wasan zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya da suka buga a birnin Durban na Afrika ta Kudu.

Hakan na nufin ta tsallake wasan kusa dana kusa da karshe inda take jiran wanda yayi nasara tsakanin Brazil ad Chile.

Ian Robben ne ya fara zira kwallo a minti na goma sha takwas da fara wasa, kuma haka aka tafi hutun rabin lokaci.

Sai dai bayan andawo Haland ta ci gaba da kai hare-hare, yayinda ita Slovakiya tayi ta kokari kare kanta.

Haka dai a ci gaba da wasa har sai a minti na 84 sannan Sneidjer ya zira kwallo ta biyu, yayinda ana minti na 94 Slovakiya ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida, inda Vittek ya zira kwallo.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Kamar yadda aka yi hasashe Holand ta dogare kan kwararrun 'yan wasan ta irin su Ian Robben wanda yayi fama da rauni da Robben Van Persie da Mark Van Vommel da

Sneidjer.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.