An sabunta: 29 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 11:18 GMT

Karawa tsakanin Paraguay da Japan

'yan wasan Japan

'yan wasan Japan sun kware wajen buga firi kik, amma Paraguay ma ba kanwar lasa bace

Duka Paraguay da Japan na neman nasara a wannan wasa domin kafa sabon tarihi a rayuwar kwallon kafa na kasashen na su.

Japan ana ta bangaren za ta so ta lashe wasan domin kaiwa zagaye na gaba akaron farko a wajen yankin Asiya.

Sannan tana fatan zamowa kasa ta farko daga nahiyar Asiya da ta taba yin nasara a kan wata kasa daga kudancin Amurka.

Yayinda ita kuma Paraguay tasha kashi a zagaye na biyu a gasar uku da aka buga a baya, abinda yasa take son ganin ta matsa gaba a wannan karon.

Paraguay za ta dogare ne akan shahararrun 'yan wasan ta irin su Roque Santa Cruz da Lucas Barrios da Nelson Valdez.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Itama Japan dai ba kanwar lasa bace, ganin yadda ta doke Kamaru da Denmark a zagayen farko.

Kuma za ta dogare ne kan 'yan wasan ta irin su Keisuke Honda da Yasuhito Endo da Kakoto Hasebe, abinda yasa masana ke ganin ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.