An sabunta: 29 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 17:27 GMT

Karawa tsakanin Spaniya da Portugal

Kasashen biyu sun buga wasa ne sau talatin da biyu a tsakaninsu, inda Portugal ta lashe wasa biyar ita kuma Spain ta lashe goma sha biyar, sanan su ka buga kunnen doki a wasa goma sha biyu.

Amma a haduwan karshe da suka yi Portugal ce ta yi nasara inda ta doke Spain da ci daya mai ban haushi a gasar cin kofin nahiyar Turai a shekarar 2004.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Spaniya dai ta doke Portugal ne sau guda a wasa goma da suka buga tarihi tun bayan shekara 1958.

Idan Spain ta samu lashe gasar cin kofin duniya, za ta kafa tarihi a matsayin kasa ta farko da ta lashe gasar wanda kuma aka doke ta a wasan farko da ta buga.

Har yanzu dai, babu dan wasan Spaniyan da aka nunawa katin gargadi a gasar.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.