Manchester City ta sayi David Silva

David Silva
Image caption David Silva ya taka rawar gani a Valencia

Manchester City ta cimma matsaya da Valencia domin sayen dan wasan gefe na Spaniya David Silva a wani farashi da ba a bayyana ba.

Manchester City da dan wasan sun cimma matsaya kan kwantiragin shekaru biyar, wanda ake saran zai kammala gwajin lafiya bayan an kammala gasar cin kofin duniya.

Yace : "Gasar Premier na daga cikin mafiya inganci a duniya, kuma ina fatan taimakawa City domin samun nasara."

"Klub ne da yake da 'yan wasa masu kyau, kuma yana da kyakkyawar makoma, kuma ina so na kafa tarihi a klub din."

Silva shi ne dan wasa na biyu da Manchester City ta dauka a 'yan kwanakin nan, bayan da ta sayi dan wasan kasar Jamus Jerome Boateng daga kungiyar Hamburg.

Shi ma kociyan Manchester City Roberto Mancini, ya yabawa Silva, yana mai cewa: "Yana daya daga cikin 'yan wasan tsakiya mafiya kyau a nahiyar Turai."

Yace: "Ina fatan zai yi mana amfani sosai, na yi farin ciki da zuwan sa, kuma zai yi tasiri matuka."

Silva ya fara buga kwallo ne a Valencia, sannan aka ba da shi aro ga kungiyoyin Eibar da Celta Vigo, kafin ya kara komawa Valencia inda ya fito da kansa, sannan har ya shiga kungiyar kwallon kafa ta kasar Spaniya.