Ghana ba ta fuskantar matsin lamba

Tawagar Ghana na horo
Image caption Tawagar Ghana na horo

Kocin Ghana Milovan Rajevac ya ce tawagar kasar ba ta fuskantar mastin lamba ganin ita ce kasar Afrika da ta rage kadai a gasar cin kofin duniya.

Tawagar Black Stars ta Ghana za ta buga wasan dab da kusa dana karshe ne da Uruguay, kuma idan ta samu nasara, za ta zama kasar Afrika ta farko da ta kai zagayen wasan kusa dana karshe a gasar cin kofin duniya.

"Ba ma fuskantar matsala domin mu kafa tarihi, amma dai muna son muyi hakan". Inji Rajevac.

"Ba zamu sauya sallon yadda muke taka leda ba, kuma ko tananin matsin lamba daga wadanda ke goyon bayan mu".

Ghana dai ta doke Amurka ne da ci biyu da guda a wasan zagaye na biyu a gasar.