Hodgson ne sabon kocin Liverpool

Sabon kocin Liverpool, Roy Hodgson
Image caption Sabon kocin Liverpool, Roy Hodgson

Roy Hodgson ne ya maye gurbin Rafeal Benitez a matsayin kocin Liverpool, bayan ya saha hannu a kwantaragin da zai sa ya jagoranci kungiyar na tsawon shekaru uku.

"Wanan wani babban aiki ne na horas da irin wanan kungiya mai girma, kuma ina matukar farin ciki da zuwa kungiyar". Inji Hodgson

Kocin mai shekarun haihuwa 62 a baya dai yana horon kungiyar Fulham ce wanda kuma ya kai ta zuwa wasan karshe a gasar Europaa a kakkar wasan bara.

Hodgson ya kama aiki ne a Fulham da ya bari a watan Disamban shekarar 2007, inda kungiyar ta samu nasarori karkashin jagorancin sa ya zuwa yanzu.