An sabunta: 2 ga Yuli, 2010 - An wallafa a 11:43 GMT

Holand ta doke Brazil da ci 2-1

Karawa tsakanin Holand ad Brazil

Holland ta doke Slovakiya a zagayen da ya gabata da ci 2-1

Holand ta doke Brazil da ci biyu da daya a gasar cin kofin duniya a filin wasa na Nelson Mandela, inda ta tsallake zuwa zagayen kusa da na karshe.

A yanzu za ta jira kasar da ta samu nasara a karawar da za a yi tsakanin Ghana da Uruguay.

Brazil ce ta fara zira kwallo a minti na goma, sai bayan an dawo daga hutun rabin lokaci sannan Holand ta rama ta hannun Melo da ya ci gida da kuma Weisly Sneijder.

Wannan shi ne karo na biyu a jere da ake cin ye Brazil a zagayen dab da na kusa da karshe, bayan da ta fita a irin wannan mataki a gasar da ta gabata.

Wannan ne karawa ta goma tsakanin kasashen biyu, inda Brazil ta lashe uku, yayinda Holand ta lashe biyu, sannan aka tashi canjaras a karo hudu.

Holand dai bata taba lashe gasar cin kofin duniya ba atarihin ta, kuma tana fatan kafa sabon tarihi a Afrika ta Kudu.

Ga dai kididdigar yadda wasan ya kaya.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.