Uruguay ta samu nasara a kan Ghana

Kasar Uruguay ta lallasa Ghana da ci 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida, abin da ya kawo karshen fatan kasashen Afrika na lashe gasar da ake gudanarwa a karon farko a nahiyar.

Nasarar da Uruguay din ta samu ya bata damar tsallakewa zuwa zagayen semi-finals wato wasan kusa da na karshe inda za ta hadu da kasar Holland.

Tun da farko sai da aka yi karin lokaci a wasan bayan an tashi kunnen doki a mintuna casa'in na farko.

Dan wasan Ghana Asamoah Gyang ya kasa cin bugun daga kai sai mai tsaron raga a mintin karshe na wasan, wanda da ya ci da Ghana ce za ta lashe wasan.

Tun da farko sai da Holland ta fidda Brazil a zagayen Quarter Finals, bayan da ta doke ta da ci 2 da 1.

Brazil dai ta taba lashe kopin har sau 5.