Dolene Spain ta kara nuna kwazo- Del Bosque

Dolene Spain ta kara nuna kwazo- Del Bosque

Kocin Spaniya Vicente Del Bosque ya amince cewar dolene 'yan wasan kasar su kara nuna kwazo muddin suna su tsallake zuwa wasan karshe a gasar cin kofin duniya.

Spaniya dai ta sha da kyar ne, bayan ta doke Paraguay da ci daya nema a wasan dab da kusa dana karshe.

"Muna shiga cikin rudu a wasan, mun sha da kyar". Inji Del Bosque.

Del Bosque ya ce tawagar Jamus ta fi kowace kwarewa a gasar.

"Muna cikin farin cikin saboda mun kai wasan kusa dana karshe" Inji Del Bosque.