Hukumar kwallon Najeriya ta sallami Shugaban ta

Hukumar kwallon Najeriya ta sallami Shugaban ta

Yayin da wa'adin da Hukumar FIFA ta ba Najeriya zai cika wanda ta umarci ta da ta soke dakatarwar data yiwa kungiyar kwallon kafa ta kasar daga shiga gasar kasa-da-kasa har na tsawon shekaru biyu, kwamitin gudanarwa na Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ya kira taron gaggawa inda ya sallami shugaban hukumar Mr. Sani Lulu da kuma mataimakinsa Amanze Ugbulam.

Kwamitin ya sake neman afuwa daga sauran 'yan Najeriya saboda mumunar rawar da tawagar kasar ta taka a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da ta halarta a kasar Afrika ta kudu.

Kwamitin har wa yau dai ya roki shugaba Goodluck Jonathan da karamar murya da ya sauya matakin da ya dauka na dakatar da 'yan wasa daga buga wasanni kasa da kasa na tsawon shekaru biyu domin gujewa fushin FIFA tare da alkawarin gyara a harkokin hukumar domin inganta harkar kwallon kafa.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne mai magana da yawun hukumar ta FIFA Nicolas Maingot ya shaidawa manema labarai cewar FIFA ta aikawa da Najeriya wasika, inda ta bata wa'adin zuwa karfe shida na ranar Litinin da ta janye matakin data dauka na hana kasar buga wasannin kasa-da-kasa har na shekaru biyu.

Hukumar ta FIFA ta ce rashin yin hakan zai sa ta dakatar da hukumar kwallon kafa ta kasar wato NFF, da kuma kin aiki da kwamitin rikon da gwamnatin Najeriya ta ce za ta kafa.

Hukuncin da Najeriya za ta fuskanta zai hada da dakatar da kasar da kuma klub klub da alkalan wasa na kasar daga wasannin da FIFA da CAF ke shiryawa, tare da dakatar da baiwa kasar kudaden shiga na FIFA da CAF.