Brazil ta kori Dunga

Carlos Dunga
Image caption Brazil bata taka rawar azo a gani a gasar ta bana ba

Brazil ta kori Carlos Dunga a matsayin kociyan 'yan kwallon kasar, bayan da suka sha kashi a hannun Holan a zagayen dab dana kusa da karshe a gasar cin kofin duniya da ake yi a Afrika ta Kudu.

Wata sanarwa daga hukumar dake kula kwallon kafa a kasar CBF, ta tabbatar da cewa an kori kociyan tare da baki dayan masu taimaka masa.

Dunga, dan shekaru 46, wanda ya koma gida ranar Lahadi tare da 'yan wasan sa, ya bayyana cewa yana tunanin barin aikin bayan da Holand ta doke su a ranar Juma'a.

Hukumar ta CBF ta ce za ta sanar da sabon kocin da zai jagoranci kasar nan da karshen wata mai zuwa.

Tuni aka fara hasashen kociyan Corinthians Mano Menezes da tsohon kocin AC Milan Leonardo a matsayin wadanda za su iya gadar mukamin.

Luiz Felipe Scolari, wanda ya jagoranci kasar ta lashe gasar kofin duniya karo na biyar a shekara ta 2002, ya ce ba zai karbi mukamin ba, saboda yana da kwantiragi da kungiyar Palmeiras.

Dunga dai yayi fice ne lokacin da ya goranci Brazil a matsayin kyaftin inda ta lashe gasar cin kofin duniya a shekarar 1994.