Caster Semenya za ta dawo tsere

Caster Semenya
Image caption Caster Semenya

'Yar tseren mita dari takwas din kasar Afrika ta kudu, Caster Semenya za ta dawo tsere bayan Hukumar tsallaye tsallaye da guje guje ta duniya wato IAAF ta wanke 'yar tseren daga tuhumar da ake yi mata.

'Yar tseren mai shekarun haihuwa 19, ba tayi tsere ba har na tsawon watanni goma sha daya saboda ana tantance gwajin da akayi mata ko cewa ita maza mata ce.

"Hukumar IAAF ta amince da bincinken da aka gudanar game jinsin Semanya, kuma a yanzu haka 'yar teren za ta iya ciki gaba da tsere". Inji sanarwa da Hukumar IAAF ta fitar.

"Muna kuma shaidawa jama'a cewa, bayanan gwajin da aka yiwa 'yar tseren zai ci gaba da zama sirri".

Semenya dai a yanzu za ta iya takara a gasar tsere da za a yi a Canada a wanan wata da kuma wadanda za a yi a gaba.