An sabunta: 7 ga Yuli, 2010 - An wallafa a 12:28 GMT

Karawa tsakanin Jamus da Spaniya

David Villa da Miroslav Klose

David Villa da Miroslav Klose sun zira kwallaye tara a gasar ta bana

A ranar Laraba ne Jamus za ta kece raini da Spaniya a wasan kusa da na karshe a ci gaba da gasar cin kofin duniya da ake yi a Afrika ta Kudu.

Wannan karawar dai wata dama ce ga Jamus na ta rama dukan da Spaniya ta yi mata a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Turai a shekara ta 2008.

Tarihi ya nuna cewa kasashen biyu sun taba karawa sau 20, inda Jamus ta samu nasara sau takwas, yayinda Spaniya ta samu nasara sau shida, sannan aka tashi canjaras a wasanni shida.

Amma akarawa uku da suka wuce tsakanin su a gasar cin kofin duniya, duka Jamus ce ta samu nasara.

Wannan ne karo na farko da Spaniya ke halartar wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya, abin da yasa take fatan kafa tarihi.

Za dai ta dogara ne kan 'yan wasan ta irin su David Villa da Iniesta da Xavi.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Ana ta bangaren Jamus wannan ne karo na sha daya da take halartar wannan matakin, kuma sau biyu aka taba samun nasara a kanta.

Jamus za ta dogara kan 'yan wasan ta irin su Klose da Podoski da Philip Lamp da kuma Ozil, amma dai za ta yi ne babu Thomas Muller wanda kawo yan zu ya zira kwalleye hudu a gasar ta bana.

Duk wanda ya samu nasara a tsakanin kasashen biyu, to Holand na nan na jiran ta domin fafatawa a wasan karshe ranar Lahadi.

A ranar Talata ne dai Holand ta doke Uruguay da ci uku da biyu, abin da ya bata damar tsallakewa zuwa zagayen karshe na gasar.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.