Ghana ta nemi a sauya dokokin kwallon kafa

Jirgin da ya kawo 'yan wasan Ghana gida
Image caption Dubban jama'a ne suka tarbi 'yan wasan na Ghana bayan sun koma gida

Kasar Ghana ta nemi hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, da ta sauya wasu daga cikin dokokin kwallon kafa, bayan da Uruguay ta fitar da kasar a gasar cin kofin duniya da ake yi a Afrika ta Kudu.

Ministan kula da harkokin wasanni na kasar, Akua Sena Dansua, ya ce wasu daga cikin dokokin kwallon ba su da wani amfani na azo a gani.

Dan wasan Uruguay Suarez ne ya taba kwallo da hannu a cikin raga a mintin karshe na wasan abin da ya hana Ghana zira kwallo.

Kuma daga baya Ghana ta zubar da fanaretin da aka bata, abin da ya baiwa Uruguay damar lashe wasan.

Gwamnatin kasar ta Ghana ta baiwa kowanne daga cikin 'yan wasan na Black Stars kyautar dala 20,000 saboda rawar da suka taka a gasar ta bana.

Ghana ce dai kasar Afrika tilo da ta tsallake zuwa zagayen na biyu na gasar, sannan ta kafawa kanta sabon tarihi, bayan da ta kai zagaye dab da na kusa da karshe.