Spain ta doke Jamus

'Yan wasan Spaniya na murnar zura kwallon da suka yi
Image caption Yanzu Spaniya za ta kara ne da Holland a wasan karshe na gasar

A cigaba da gasar cin kopin duniya na kwallon kafa da ake yi a Afrika ta Kudu, dazu Spaniya ta doke Jamus da ci 1 mai ban haushi a wasan kusa da na karshe a birnin Durban.

Wannan ne karo na farko da Spaniya ke halartar wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya, abin da ya sa ta kafa tarihi.

Spaniya dai tana rike da kopin kasashen Turai inda ta yi nasara kan Jamus a shekara ta 2008.

Yanzu dai Spaniya za ta kara da Holand a wasan karshe ranar Lahadi.

Ranar Asabar kuwa zaa kece reni tsakanin Jamus da Uruguay don samun kasar da za ta kasance ta uku a gasar.