FIFA za ta sauya tsarin alkalanci

Kwallon da Lampard ya zira
Image caption Wannan Kwallon da Lampard ya zira ta jawo kace-nace sosai da sosai

Ana kara tattaunawa kan amfani da fasahar zamani wajen tantance shigar kwallo a raga, bayan da hukumar FIFA tace za a sauya tsarin alkalin wasa daga gasar cin kofin duniya ta bana.

Babban sakataren FIFA Jerome Valcke, ta gayawa BBC cewa, hotunan talabijin sun nuna cewa kwallon da Frank Lampard ya zira ta shiga raga, kuma wannan "mummunar rana ce ga hukumar ta FIFA." Sannan yace za a yi sauye-sauye kafin gasar shekara ta 2014 a Brazil.

"Muna duba yiwuwar yadda za a gane kwallon da aka zira ba tare da alkalin wasa ya gani ba, don haka muke magana a kan amfani da na'urar zamani 'wato goal line technology' a turance," a cewar Valcke.

Duk da cewar wasu na ganin kalaman nasa a matsayin sauyin manufa kan matsayin hukumar a baya, babban sakataren na son a kawo sauyi a harkar alkalancin baki daya.

A baya dai shugaban FIFA Sepp Blatter, ya ki amincewa da amfani da na'urar zamani ko kuma hotunan talabijin wajen tantance kwallo, yana mai cewa dan adam ajizi ne.

Abin jira agani dai shi ne irin sauye-sauyen da hukumar za ta bullo da su, adaidai lokacin da jama'a ke kara matsa mata lamba, musamman ganin rin kuskuren da aka samu a gasar ta bana.