An sabunta: 10 ga Yuli, 2010 - An wallafa a 16:34 GMT

Jamus ta lallasa Uruguay da ci uku da biyu

Jamus ta lallasa Uruguay da ci uku da biyu a wasan da suka yi na neman kasar da za ta kasance ta uku a gasar cin kofin duniya.

Kasashen biyu dai ba bakin karawar bane, domin kasar Jamus, wadda ta taba lashe gasar cin kofin duniya har sau uku, da Uruguay, wadda ta taba lashe gasar har sau biyu, sun taba haduwa a shekarar 1970, a kokarin samun mataki na uku a gasar.

Wannan dai shi ne karo na goma da kasashen biyu suka hadu da juna. Kasar Uruguay ta samu nasara a karawar su ta farko, inda ta lallasa Jamus da ci hudu da daya a shekarar 1928, sai dai ba su sake samun nasara a kan Jamus ba.

Jamus ta samu nasara a karawa bakwai, suka yi kunnen doki a karawa daya sannan Uruguay ta samu nasara a karawa daya.

Kasar Jamus ce dai ta samu nasara a karawar da aka yi tsakanin kasashen biyu a shekarar 1993, kuma an tashi ne da ci biyar ba ko daya.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.