Dawowar Cudicini ya farantawa Redknapp rai

Harry Redknapp
Image caption Kocin Tottenham, Harry Redknapp

Kocin Tottenham Harry Redknapp ya ce ya na matukar farin ciki da dawowar taka ledan mai taron gidan kungiyar, Carlo Cudicini bayan ya dauki tsawon watanni shida yana jinya sakamakon hadarin babur da ya yi.

Kungiyar Spurs dai ta doke wata kungiya da ke taka leda a gasa ta daya a Ingila da ci hudu da nema, inda Cuducini ne ya kamawa kungiyar kwallo.

Cudini dai bai taka leda ba tun a watan Nuwamban bara.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 36, ya samu raunin ne a kugunsa da kuma hanunsa a lokacin da ya yi hatsarin.

Redknapp ya shaidawa shafin intanent din kungiyar cewa; "Ina matukar farin ciki cewar dan wasan ya warke, kuma zai taimaka mana".

Cudicini wanda tsohon dan wasan Chelsea ne ya sa hannu a kwantaragin a watan Mayun da ya gabata domin takawa kungiyar leda har zuwa shekarar dubu biyu da goma sha daya.