Mosimane ne sabon kociyan Afrika ta Kudu

Tawagar Bafana Bafana
Image caption Tawagar Bafana Bafana bata taka rawar gani a gasar cin kofin duniya ba

Hukumar kula da kwallon kafa ta Afrika ta Kudu ta nada Pitso Mosimane a matsayin kociyan kungiyar kwallon kafa ta kasar wato Bafana Bafana.

Mosimane wanda shi ne tsohon mataimakin kociyan kasar Carlos Alberto Parreira, a gasar cin kofin duniya ya sa hannu kan kwantiragin shekaru hudu.

Babban aikin da ke gaban sa dai shi ne ya kai kasar gasar cin kofin kasashen Afrika a shekara ta 2012 a kasashen Gabon da Equatorial Guinea, da kuma wanda za a yi a Libya a shekara ta 2013.

Yarjejeniyar har ila yau ta hada da kai kasar zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil a shekara ta 2014.

"Na ji dadi sosai, ganin cewa na samu ci gaba zuwa cikakken mai horas da 'yan wasa," kamar yadda sabon kociyan ya bayyana lokacin da ake gabatar da shi a birnin Johannesburg.