Ana tahumar Ribery da Benzema

Karim Benzema da Franck Ribery
Image caption Karim Benzema da Franck Ribery

'Yan sanda a Faransa na binciken 'yan wasan kasar biyar wato Franck Ribery da kuma Karim Benzema bisa zargin su da nema ta'amalin 'yan mata masu zaman kansu da shekarun su basu kai goma sha takwas ba.

Hukumar 'yan sandan kasar dai ta ce idan ta samu 'yan wasan da laifi za ta gurfanar da su a gaban kotu.

'Yan wasan dai sun musanta zargin da ake yi musu.