Cech ba zai taka leda ba na tsawon wata guda

Petr Cech
Image caption Petr Cech

Mai tsaron gidan kungiyar Chelsea Petr Cech ba zai fara wasa ba a kakar wasan bana a gasar Premier ta Ingila saboda ya samu rauni a lokacin da ya ke horo ranar talata.

Cech ba zai taka leda ba na tsawon wata guda wanda kuma zai sa dan wasan ba sai samu buga wasanni share fage na zumunta da kungiyar za ta buga kafin a fara sabon kakar wasa da kuma na kofin Community Shield da Manchester United a ranar 8 ga watan Augusta.

Chelsea dai za ta buda wasan ta na farko ne da kungiyar Wes Brom a ranar 14 ga watan Augusta.

Dan wasan dai ya samu rauni makamancin hakan a kakar wasan bara inda kuma bai taka leda ba na tsawon wata guda.