Jol ya ce ba zai koma Fulham ba

Martin Jol
Image caption Martin Jol ya jagoranci Tottenham a Ingila kafin ya bar kasar

Martin Jol ya ce ba ya bukatar komawa Ingila domin horon kungiyar Fulham a yayinda ya ce zai ci gaba da aikin da kungiyar Ajax.

Fulham dai ta dade tana tattaunawa da Ajax game da diyyar da za ta ba kungiyar game da siyan Martin Jol amma kungiyoyin biyu sun kasa cimma matsaya.

Jol, mai shekarun haihuwa 54, ya fara amincewa zai koma kungiyar ta Fulham amma daga bisani sai ya sauya ra'ayin sa.

"Ajax ta nemi da kadda in tafi kuma na kamata ya yi a tsaya a kungiyar". In ji Jol .

"Na zo kungiyar a bara in samu nasara kuma in gina kwararen kungiya, ina so in cimma wadanan bukataun a kakar wasa mai zuwa".