Newcastle ta sayi Dan Gosling

Dan Gosling
Image caption Dan Gosling ya buga wasanni 22 a Everton tun zuwansa a watan Janairun shekara ta 2008

Kungiyar Newcastle ta sayi dan wasan tawagar 'yan kasa da shekaru 21 ta Ingila, Dan Gosling har na tsawon shekaru hudu.

Dan wasan mai shekaru 20, ya samu damar barin Everton ne bayan da kwantiraginsa ta kare a tsakiyar watan Mayu.

"Wannan abu ne mai mahimmanci a gare ni, na dade ina jiran wannan rana, a cewar Gosling, kamar yadda ya shaidawa shafin intanet na Newcastle.

"Na buga wasa a filin St James' Park, kuma na son irin yadda filin ya ke kayatarwa."

Ya kara da cewa sanya jesin Newcastle wani mafarki ne da ya zamo zahiri a gareshi, zan yi murna sosai ranar da zan taka leda a gaban 'yan kallo dubu 55.