Tottenham za ta lashe gasar Premier- In ji Redknapp

Harry Redknapp
Image caption Harry Redknapp

Kocin Tottenham Harry Redknapp ya ce yana da kwarin gwiwa cewar kungiyarsa za ta lashe gasar Premier a kakar wasan bana.

Kocin mai shekarun haihuwa 63 ya kafa tarihi da kungiyar Tottenham inda ta kare a matsayin ta hudu a gasar Premier da aka yi a bara wanda kuma ya sa kungiyar ta samu gurbin a gasar zakarun Turai, da za a yi a badi.

Redknapp ya ce yana da kwarrarun 'yan 'yan wasan da za su iya lashe gasar ta Premier.