Aston Villa za ta sayar da Milner

James Milner
Image caption Milner ya taka leda sosai a gasar cin kofin duniya ta bana

Kociyan Aston Villa Martin O'Neill, ya ce a shirye yake ya sayar da dan wasan Ingila James Milner, bayan da dan wasan ya nuna sha'awarsa ta barin kungiyar.

Dan wasan na Ingila, wanda ya zo Villa daga Newcastle a kan fan miliyan 12 a shekara ta 2008, an ta kai kawo a kansa tsakanin kugiyar da Manchester City.

Villa ta sayar da shahararren dan tsakiyar nan Gareth Barry a kan fan miliyan 12 zuwa Manchester City bara.

Aban gare guda kuma ana danganta Aston Villa da neman dan wasan West Ham Scott Parker idan har Milner ya barsu a kakar wasanni ta bana.