Eriksson na son komawa Ingila

 Sven-Goran Eriksson
Image caption Eriksson na kan gaba a wadanda ake saran za su gaji Roy Hodgson a Fulham

Tsohon kociyan Ingila Sven-Goran Eriksson, wanda ake alakantawa da Fulham, ya ce yana sha'awar komawa gasar Premier ta Ingila.

Eriksson ne ake saran zai maye gurbin Roy Hodgson a Fulham bayan da suka kasa cimma matsaya da Martin Jol na Ajax.

"Wannan dama ce mai kyau, bawai kawai ga Eriksson ba, amma babu wata magana da bangarorin biyu suka yi kawo yanzu," a cewar Athole Still, mai taimakawa Ericksson.

Shi dai Ericksson ba shi da wata kungiya a yanzu, bayan da ya jagoranci Ivory Cost zuwa gasar cin kofin duniya da aka kammala a Afrika ta Kudu. An dai kore shi ne daga aiki a klob din Manchester City a shekara ta 2008, lokacin kungiyar na hannun tsohon Fira ministan Thailand Thaksin Shinawatra.

Matakin da yace yana da alaka da dangantakarsa da Mista Shinawatra, ba wai rashin kokarin kungiyar ba.