An dakatar da 'yan wasan Faransa

Tawagar 'yan wasan Faransa
Image caption 'Yan wasan Faransa sun yi bore lokacin gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu, kuma babu ko daya da zai buga wasa na gaba da kasar za ta yi.

Hukumar kula da kwallon kafa ta Faransa ta dakatar da baki dayan 'yan wasa 23 da suka halarci gasar cin kofin duniya daga wasan da kasar za ta buga da Norway.

Sabon kociyan kasar Laurent Blanc ne ya bukaci kada a gayyaci ko daya daga cikin 'yan wasan, a wasan sada zumuntar da kasar za ta kara da Norway a ranar 11 ga watan Agusta a birnin Oslo.

Faransa ta kasa cin wasa ko daya a wasanni ukun da ta buga a gasar cin kofin duniyar da aka kammala a Afrika ta Kudu.

A lokacin gasar ta Afrika ta Kudu 'yan wasan dai sun kauracewa atisayi domin goyon bayan Nicolas Anelka, wanda aka kora gida bayan ya nuna rashin da'a ga kociyan kasar Raymond Domenech.

Laurent Blanc ya ce: "Ba zan iya kawar da kai abisa abin da ya faru a Afrika ta Kudu ba."

"Na sa ido kan abubuwan da suka faru cikin damuwa, raina ya baci sosai kuma ban ji dadin wasu daga cikin halayyar da aka nuna ba."