Drogba ba zai taka leda ba a fafatawa da United

Drogba
Image caption Drogba ya ci kwallaye 37 a kakar wasan data wuce

Da alamu dan wasan Chelsea Didier Drogba ba zai taka leda ba a farkon kakar wasa mai zuwa saboda tiyatar da aka yi mishi.

Kungiyar Chelsea ta ce an samu nasarar yiwa dan wasan fida kuma ana saran bayan makwanni uku masu zuwa ya koma horo.

Abinda kuma hakan ke nufi shine Drogba mai shekaru 32 ba zai buga wasa cin kofin Charity ba tsakanin Chelsea da Manchester United a ranar takwas ga watan Agusta kafin a fara gasar premier.

Drogba dai ya kasance daya daga cikin zakarun 'yan kwallon Chelsea tun bayan da ya bar Marseille a watan Yulin shekara ta 2004 akan pan miliyan 24, kuma a kakar wasan data wuce, Drogba ya zira kwallaye 37 abinda kuma ya taimakawa Chelsea ta lashe gasar premier da ta FA.