Najeriya ta doke Amurka a kwallon mata

Falconets
Image caption 'Yan kwallon mata na Najeriya

Najeriya ta tsallake zuwa matakin kusada karshe a gasar cin kofin duniya ta mata 'yan kasada shekaru 20 bayan ta doke Amurka daci 4 da 2 a bugun penariti.

'Yar Amurka Amber Brooks ce ta fara zira kwallon farko kafin Helen Ukaonu ta farkewa Najeriya kwallon a minti na 79 abinda kuma yasa aka shiga karin lokaci bayan an tashi wasa kunen doki.

A yanzu dai Najeriya zata hadu da Columbia a ranar Alhamis a wasan zagayen kusada karshe bayan Columbia ta doke Sweden daci biyu da nema a zagayen gabda na kusada karshe.