Guti zai bar Real Madrid

Guti
Image caption Guti ya zira kwallaye 86 a Real Madrid

Dan wasan Real Madrid na tsakiya Guti ya sanarda cewar zai bar kungiyar ya koma Besiktas ta kasar Turkiya.

Guti me shekaru 33, ya fara bugawa Madrid kwallo tun a kungiyarta na matasa a shekarar 1985.

Yace "zan bar Real Madrid duk da cewar jama'ar garin na sona matuka".

A cikin jerin 'yan wasan Madrid na yanzu, Raul ne kadai ya riga Guti zuwa kungiyar.

Guti dai ya fara takawa babbar kungiyar Madrid ne a shekarar 1995 kuma ya taka mata leda sau 542 inda ya zira kwallaye 86, kuma ya lashe gasar La Liga sau biyar da kofin zakarun Turai sau uku.

Idan har Guti ya koma Besiktas, to zai hade da tsohon kocinsa Bernd Schuster.