City ta sayi Kolarov akan pan miliyan 16

kolarov
Image caption Aleksander Kolarov

Manchester City ta kamalla kulla yarjejeniya da Aleksander Kolarov daga Lazio akan pan miliyan 16.

Dan shekaru 24 da haihuwa, Aleksander Kolarov dan kasar Serbiya ya samu izinin taka leda a Ingila kuma zai yi takara ne da Wayne Bridge a bangaren hagun baya na City.

Koc Roberto Mancini ya ce "burina shine in samu zaratan 'yan wasa biyu a kowanne bangare".

Da dama na kallo Kolarov a matsayin Roberto Carlos na Brazil saboda irin karfin bugun shi da kafar hagu.