Watakila James Milner ya cigaba a Villa

Milner
Image caption Milner na daga cikin 'yan wasan da Aston Villa ke ji dasu

Manajan Aston Villa Martin O Neill ya tattauna da James Milner a ranar litinin akan batun makomar dan wasan.

O'Neill ya bayyana cewar a makon daya gabata Milner ya nuna alamun barin kungiyar don komawa Manchester City.

Sai dai wannan tattaunawar tayi armashi saboda kungiyar ta sasanta batun tsakaninta da Milner din.

A don haka dai Milner zai hade da sauran 'yan wasan Villa a horo na musamman da zasu yi a kasar Portugal.

Amma dai dan wasan ba zai buga wasan sada zumunci ba tsakanin Aston Villa da Walsall a ranar talata.