Raul ya koma Schalke 04

Raul
Image caption Raul gwarzo ne a Real Madrid

Tsohon dan kwallon Spain Raul ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya da kungiyar Shelke 04 ta kasar Jamus. Abinda ya kawo karshen shekarun da ya shafe yana taka leda a Real Madrid.

A makon da ya gabata ne dan wasa ya bada sanarwar cewa zai bar kungiyar Real Madrid bayan shafe shekaru 18 yana taka mata leda.

Raul, dan shekaru 33, ya taimakawa Real Madrid ta lashe gasar cin kofin zakarun Turai sau uku da kuma gasar La Liga sau shida, kuma shine dan kwallon daya fi kowanne zira kwallo a kasar Spain inda yaci kwallaye 44 cikin wasanni 102 daya buga mata.

Raul dai ya koma Real ne a shekarar 1992 kuma a watan Oktoban 1994 yana shekaru 17 ya buga mata wasan farko tsakaninta da Real Zaragoza, kuma cikin wasanni 741 daya bugawa Real ya zira kwallaye 323.

Dan wasan dai ya bayyana cewa ba a son ransa ya bar kungiyar ta Real Madrid ba.

Raul ya bi sahun Guti wanda ya koma kungiyar Turkiyya, wajen shiga sahun tsofaffin 'yan wasan Real Madrid da suka barta a 'yan kwanakin nan.