Bonetti ne sabon kocin Chipolopolo

Bonetti
Image caption Dario Bonetti zai jagoranci Chipolopolo har zuwa 2012

Hukumar kwallon kafa ta kasar Zambiya ta tabbatar da nadin tsohon dan wasan Juventus Dario Bonetti a matsayin kocin Chipolopolo.

Bonetti ya maye gurbi Herve Renard wanda yayi murabus a watan Maris daya wuce.

Bonetti mai shekaru 48 a baya ya takawa Roma da AC Milan leda kuma ya taba zama kocin Hungary da Scotland da kuma Romania.

Kakakin hukumar kwallon Zambia Emmanuel Munaile ya shaidawa BBC cewar Bonetti ya kulla yarjejeniya ta tsawon shekaru biyu.