Bolton ta sayi Alonso daga Real Madrid

Bolton
Image caption Tambarin kungiyar Bolton

Bolton ta kulla yarjejeniya da dan wasan Real Madrid Marco Alonso na tsawon shekaru uku.

Dan shekaru 19 da haihuwa, Alonso a bugawa Real Madrid wasanshi na farko ne a watan Aprilu a wasa tsakaninsu da Racing Santander.

Kocin Bolton Owen Coyle yace " matashin dan wasa ne wanda yake da baiwa sosai".

Alonso ya kasance dan kwallo na uku da Bolton ta siya kafin a fara kakar wasa ta bana.