Mascherano zai bar Liverpool

Mascherano
Image caption Mascherano yana gurmuzu da dan wasan Athletico Madrid

Kocin Liverpool Roy Hodgson ya tabbatar da cewar dan wasan tsakiya Javier Mascherano na son ya bar kungiyar.

Dan kwallon na Argentina mai shekaru 26 ana tunanin zai koma kungiyar Inter Milan don ya hade da tsohon kocinsa Rafael Benitez.

Mascherano bayan ya dawo daga hutun gasar cin kofin duniya ya shaidawa Hodgson cewar zai bar kungiyar.

A cewar Hodgson"ya gaya mani cewar yana son ya barmu amma dai yarjejeniya tsakaninmu sai a shekara ta 2012 ne zata kare".