Rangers zata sayi 'yan kwallon Afrika ta Kudu biyu

Bafana bafana
Image caption Wasu magoya bayan kasar Afrika ta Kudu

Shugaban kungiyar Rangers Martin Bain ya fara tattauna don sanyen wasu 'yan kwallon Afrika ta Kudu Bongani Khumalo da Katlego Mphela.

A cewar kungiyar ta Rangers ta Scotland Manajanta Walter Smith ya zaku ya sayi Khumalo mai shekaru 23 da kuma Mphela mai shekaru 25.

Duka 'yan wasan biyu dai sun zira kwallo a wasan da Afrika ta Kudu ta doke Faransa kuma ana saran za a biya pan miliyan daya da rabi akan kowanne dan wasan.

Khumalo dai shine Kaptin din Supersport United a yayinda Mphela shine dan wasan daya fi kowanne zira kwallo a kakar wasan data wuce a Afrika ta Kudu.