Campbell zai koma Newcastle

Sol Campbell
Image caption Sol Campbell ya dade yana taka leda a gasar Premier

Rahotanni na nuna cewa Newcastle United na gab da daukar tsohon dan wasan Ingila Sol Campbell, bayan da dan wasan ya je klob din domin gwajin lafiya ranar Talata.

Dan wasan mai shekaru 35, ya zamo ba shi da kwantiragi bayan da yarjejeniyarsa da Arsenal ta kare a karshen kakar wasanni ta bara.

Rahotannin sun nuna cewa Arsenal ta yi kokarin ganin ta ci gaba da rike dan wasan.

Amma dan wasan ya nuna alamun yana so ya koma Newcastle, a shirye-shiryen da suke yi na turkarar gasar Premier ta bana, bayan da suka dawo daga Championship. Campbell zai zamo dan wasa na uku da kungiyar Newcastle ta dauka a bana, bayan da ta sayi Dan Gosling da James Perch.

Shi dai manajan Newcastle Chris Hughton, yana so ne ya karfafa 'yan bayansa, adaidai lokacin da yake sauraron tasirin raunin da Steven Taylor ya samu.