Kocin Faransa Blanc ya ce zai yi murabus

Blanc
Image caption Blanc na cikin 'yan kwallon Faransa da suka lashe kofin duniya a 1998

Kocin Faransa Laurent Blanc ya ce zai yi murabus kafin karshen kwangilarshi da Faransa ta kare idan har ya kasa samun gurbin zuwa gasar cin kofin kasashen Turai na shekara ta 2012.

Blanc dai ya maye gurbin Raymond Domenech ne a matsayin kocin Faransa bayan da kasar ta kasa taka rawar gani a gasar cin kofin duniya da aka yi a Afrika ta Kudu.

Blanc yace" buri na shine gasar Euro 2012, kuma idan har ban tsallake ba tabbas zan ajiye mukamin".

Kocin Faransan dai ya kulla yerjejeniya ta tsawon shekaru biyu ne da kasarshi wacce ya taimakawa ta lashe gasar cin kofin duniya a shekarar 1998.