Ike Uche ya kara turgudewa

Ike Uche
Image caption Ciwon gwiwa ne ya hana Uche zuwa Afrika ta Kudu

Dan kwallon Najeriya Ikechukwu Uche ya kara samun sabon rauni abinda kuma ke nufin ba zai buga wasan sada zumunci tsakanin Super Eagles da Koriya ta Kudu ba.

Sai dai dan wasan Real Zaragoza din na fatar cewa dashi za a fara taka leda a farkon kakar wasa ta La Liga da za a fara a karshen watan Agusta.

A kakar wasan data wuce dai Ike Uche yayi ta fama da ciwon gwiwa har sai da aka yi mashi tiyata abinda kuma ya sanya bai shiga cikin jerin 'yan kwallon da suka wakilci Najeriya ba a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu.