Maradona ya bar Argentina

Diego Mardona
Image caption An ta rade-radi kan makomar Diego Mardona tun bayan gasar cin kofin duniya

Hukumar kwallon kafa ta kasar Argentina ta tabbatar da cewa Diego Maradona ba zai ci gaba da horas da tawagar kwallon kafa ta kasar ba. Maradona, dan shekaru 49, ya bayyana cewa yana so ya ci gaba da aikin nasa, a lokacin da yake gab da tattaunawa da shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Julio Grondona ranar Litinin.

Amma bayan da Maradona ya ki amincewa da ya sauya masu taimaka masa, sai hukumar kwallon taki amincewa ta kulla sabuwar yarjejeniya da shi.

A yanzu hukumar ta umarci kociyan 'yan kasa da shekaru 20 na kasar Sergio Batista, ya ci gaba da rike tawagar na wucin gadi. An faitar da Argentina a zagayen dab da kusa dana karshe na gasar cin kofin duniya, inda ta sha kashi a hannun Jamus da ci hudu da nema. Grondona ya ce: "An kasa cimma matsaya, cikas din da aka samu shi ne na kin amincewar Maradona, na ya sauya masu taimaka masa." Amma ya ce ba korar Maradona a ka yi ba. Kawai dai ba'a sake kulla yarjejeniya da shi bane.