Fabregas ba zai bar Arsenal ba- Wenger

Arsene Wenger
Image caption Kocin Arsenal Arsene Wenger

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ja layi akan cecekucen da ake tayi akan makomar Cesc Fabregas a kungiyar, inda yace Kaptin din bana sayarwa bane.

A watan Yuni ne, Barcelona ta taya Fabregas akan pan miliyan 29, amma Arsenal taki amincewa.

Wenger yace" Cesc dan wasa ne mai mahimanci gaske gare mu, shine kaptin din mu saboda haka baza mu sake shi ba".

Duk da cewar Barca ta fidda maitarta a fili don ta sayi Fabregas, amma dai kakakin Barca din Toni Freixa ya ce mahukunta a Arsenal sunki zama dasu.