Beckham ya ce bazai koma West Ham ba

Beckham
Image caption Tsohon kaptin din Ingila David Beckham

Tsohon kaptin din Ingila David Beckham ya ce baida niyyar barin kungiyar Los Angeles Galaxy ta Amurka don ya koma kungiyar West Ham ta Ingila.

Mai magana da yawun Beckham din ya karta rahotannin dake cewar Beckham din na tattaunawa da canza sheka zuwa West Ham.

David Gold daya daga cikin mahukunta West Ham ne ya bayyana cewar suna tattaunawa da ajen din David Bechkam akan yiwayar sayen dan wasan.

A halin yanzu dai Beckham din yana murmurewa daga raunin da ya samu abinda kuma ya hanashi zuwa gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu.