Najeriya za ta kara da Jamus a wasan karshe

Falconets
Image caption 'Yan kwallon mata na Najeriya wato Falconets

Najeriya da Jamus sun tsallake zuwa wasan karshe na gasar kwallon duniya ta mata 'yan kasada shekaru 20 da ake bugawa a Jamus.

Najeriyar dai a karon farko a tarihi ta samu gurbin ne bayan ta samu galaba akan Columbia daci daya me ban haushi a wasan zagayen kusada karshe.

Minti biyu kacal da fara wasan ne 'yar Najeriya Joy Jegede da gwada golar Columbia daga nesa sannan sai Ebere orji ta zira kwallon data like har aka tashi wasan.

Jamus ta lallasa Koriya ta Kudu ne daci biyar da daya, inda Alexander Popp taci kwallaye biyu a daya wasan kusada karshe.

Wannan nasarar da ya nuna cewar Jamus mai saukin baki zata kara da Najeriya a wasan karshe na gasar a ranar daya ga watan Agusta a yayinda Koriya ta kudu zata kece raini da Columbia don neman zama na uku.