Dan kwallon Jamus Khedira zai koma Real

Sami Khedira
Image caption Matashin dan kwallon Jamus Sami Khedira

Dan kwallon Jamus wanda ke takawa Stuttgart leda Sami Khedira na gabda kumawa kungiyar Real Madrid ta Spain.

Darektan wasanni na Stuttgart Fredi Bobic wanda ya tabbatar da haka ya ce "tabbas mun samu tayi daga wajen Real akan dan wasan, yanzu dai yarjejeniya ce ta rage".

Khedira dai na daga cikin 'yan wasan da suka haskaka a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu inda Jamus ta zama ta uku, kuma kwangilarshi da Stuttgart zata kare ne a shekara ta 2011.

Rahotanni sun nuna cewar Stuttgart na shirin barin dan kwallon ya koma Real Madrid akan Euro miliyan 15, a yayinda ita kuma Real din ta taya dan wasan akan Euro miliyan 8 zuwa 10.