David James ya koma Bristol

David James
Image caption David James

Kungiyar Bristol City da ke gasar Championship a Ingila ta sayi mai tsaron gidan tawagar Ingila, David James daga kungiyar Portsmouth.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 39, ya sa hanu ne a kwantaragin shekara guda, amma yana da damar kara wa'adin wani shekaran idan yana so.

James, ya bugawa Ingila wasa sau 53, kuma ya baro kungiyar Portsmouth ne bayan kwantaraginsa ya kare.

A baya dai anyi hasashen cewar dan wasan zai koma kungiyar Fulham ko Sunderland.

James, dai ya tattauna da kungiyar Celtic, amma dan wasan da kungiyar ba su cimma matsaya ba.