Liverpool ta yi nasara a gasar Europa

David Ngog
Image caption David Ngog

David Ngog ne ya zura kwallaye biyu inda Liverpool ta yi nasara a kan kungiyar Rabotnicki a wasan shara fage zagaye na uku a gasar Europa.

A wasan shi na farko da ya jagoranci kungiyar, sabon kocin Liverpool Roy Hodgson bai yi amfani da manyan 'yan wasa shi su goma da su ka taka leda a gasar cin kofin duniya da aka kammala a kasar Afrika ta kudu ba, daga ciki ma har da kyaftin din kungiyar Steven Gerrard.

Roy Hodson ya ce yana da kwarin gwiwa a kan 'yan wasan da yake da su, inda ya ce za su taka rawar gani a kakar wasan bana.

Kocin dai a baya ya soki matakin da hukumar Uefa ta dauka na sanya Liverpool ta buga wasanni share fagen taka leda a gasar Europa bayan wasu 'yan kwanaki da aka kamalla gasar cin kofin duniya.