Uche ba zai taka leda ba na tsawon wata uku

Ikechuckwu Uche
Image caption Ikechuckwu Uche

Dan wasan Najeriya Ikechukwu Uche zai dauki watanni uku yana jinya sanadiyar raunin da ya samu.

Banya anyiwa dan wasan aikin tiyata aka tabbatar masa cewar ba zai samu buga wasa ba na wani tsawon lokaci.

"Gaskiya ban ji dadin wanan lamarin ba, saboda da farko da aka duba raunin an ce ba zan dade inda jinya ba". In ji Uche.

A kakar wasan data wuce dai Ike Uche yayi ta fama da ciwon gwiwa har sai da aka yi mashi tiyata abinda kuma ya sanya bai shiga cikin jerin 'yan kwallon da suka wakilci Najeriya ba a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu.